Om Bangaskiya bisa Kamili
Mene Allah Ya ke bukata daga wurin mu? Wannan tambaya ne da dukan mu na gwagwarmaya da shi, mu na tunanin akwai wani abu musamman da yakamata mu yi domin mu samu amincewan Allah.
Abram Ya amince da Ubangiji, Ubangiji kuwa ya lasafta
wannan adalci ne a gare shi. - Farawa 15:6
Allah a kullum na bukatan bangaskiyan mu. Ya bukaci Adamu da Hauwawu su badagaskiya cewa dokokin Shi na kyau kuma na da amfani bi. Ya bukaci Nuhu ya dogara gare Shi kuma ya gina jirgin ruwa domin ya ceci iyalin shi. Kuma Ya umurce Abram ya bar gidan su da iyalin shi kuma ya je kassan da Allah zai nuna mashi.
A yau, Allah Ya na umurce mu mu sa bangaskiyan mu a cikin aikin ceton na ¿an Shi, Yesu Almasihu, domin ceton mu da bukatun mu. Ya bukace mu mu dogara gare Shi domin rayuwan mu na har abada da na kullum. Idan mun badagaskiya cewa Yesu Ya mutu domin zunuban mu kuma muna biyyaya da dokokin Shi, muna tafiya cikin bangaskiya. Allah bai sa dole mu za da kamili ba, kawai Ya bukaci mu yi tafiya da Shi a cikin bangaskiya da Shi.
Idan muna shakkan abin da Allah Ya bukace mu mu yi, muna iya binciken rayuwan mutanen Allah kuma mu duba misalen bangaskiyan su. Bangaskiya bisa Kamili na duban rayuwan Abran (daga baya ya zama Ibrahim) da ¿an Shi Ishaku. Ibrahim da Ishaku ba masu kamili ba ne. Allah Ya basu duk wani babban alkawali, amma akwai lokatai da dama da ayukan su bai nuna bangaskiyan su ba. Allah Ya lisafta wa Ibrahim wannan adalaci a gare tun däewa kamin Ya bukaci wani abi daga gare shi ban da bangaskiya.
Mu häa kai a yanan gizo domin wannan binciken na tsawon mako shida ko kan app namu na Love God Greatly. Can za ki samu abubuwan da ya shafi Bangaskiya bisa Kamili a wannan wurare biyutare da rubuce rubucen mu na Litinin, Laraba da Jumma'a, da karin bayani ta wurin karatu na kullum da jamma'a masu kauna domin karfafa mu yayin da mu ke binciken rayuwan Ibrahim da Ishaku da abin da ake nufi a yi rayuwan bangaskiya.
Vis mer