Om Cikin Yesu ki ke
Ni wanene? Menene ya sa ina nan? Akwai amfani na?
Duk wannan tambayoyi ne da dukan mu mun yi a wani lokaci. Yayinda mu tafiya cikin rayuwa mu na so mu gane ko mu wanene, menene ya sa an halice mu, da kuma menene amfanin wannan rayuwan. Ba za mu iya amsa wannan tambayoyin ba tare da gane ko mu wanene ba.
Idan ba mu gane mu wanene ba, ba za mu iya yin rayuwa yadda a kera mu mu yi ba. Ya na da saukin yin tunanin ko mu wanene bisa ga iyalin mu, aikin mu, abokan mu, abin muke son yi ko kasan mu. Yawance muna tunanin mu wanene ta wurin ayukan mu, ko kalmomin mu ko halin mu.
"Saboda haka, duk wanda yake na Almasihu sabuwar halitta ne, tsohon al'amari duk ya shu¿e, ga shi, kome ya zama sabo." -2 Korantiyawa 5:17
A cikin Almasihu ne käai mu gane ko mu wanene. Komin yaya mu ka yi tunanin kan mu, sanin ko mu wanene a cikin Almasihu ¿aya ne. Ya cice mu daga zunubi, Ya kubutas da mu daga duhu kuma Ya fashe mu daga kunya. Ta wurin Shi ana kiran mu 'ya'yan Allash, wanda aka ¿auke mu cikin iyalin Allah kuma aka mayar da mu 'yan kasan mulkin Almasihu. A cikin Almasihu, mun samu ceto, hatimi, gafara, zäe, albarka da karfafawa.
A cikin Yesu ki ke: Sanin ko mu wanene a cikin Almasihu wani binciken Littafi mai Tsarki ne na tsawon mako hu¿u akan sanin ko mu wanene a cikin Almasihu. Ta wurin sa karfin kan gaskiyan sanin mu wanene a cikin Yesu, da abin da Ya bamu ta wurin häayan Shi, da yadda mu samu hatimi a zama 'ya'yan Shi, za mu gane ainihin mu wanene. Yayin da mu ke girma cikin bangaskiyan mu za mu iya girma cikin tabbaci da amincewan mu wanene a cikin Shi.
Mu häa kai a yanan gizo domin wannan bincike na tsawon mako hu¿u ko kan app namu na Love GOD Greatly. A can za ki samu abubuwan da sun shafi A cikin Yesu ki ke a duka wurare biyu tare da rubuce rubucen mu na Litinin, Laraba da Jumma'a, da karin bayyanita wurin karatu na kullum da kuma jamma'a ma su kauna domin karfafa ki yayinda ki ke binciken ma'anansamun tushen mu a cikin Yesu.
Vis mer